1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Falasdinu zai kai ziyara zuwa Rasha

August 11, 2024

A ranar Litinin ake sa ran shugaban Falasdinu, Mahmud Abbas zai kai ziyara Moscow domin ya gana da Shugaba Vladmir Putin na Rasha a kan yakin Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4jLtt
Shugaba Vladmir Putin na Rasha da kuma Mahmud Abbas na Falasdinu
Shugaba Vladmir Putin na Rasha da kuma Mahmud Abbas na FalasdinuHoto: YEVGENY BIYATOV/AFP

Ana dai ganin shugaban Rasha, Vladmir Putin da na Falasdinu, Mahmud Abbas za su  tattauna kan abubuwan da suka biyo bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar bakwai ga watan Octobar bara, da kuma irin rawar da Rasha za ta iya takawa a yakin.

Shi dai Abbas shi ne ke shugabantar kungiyar Fatah da ke adawa da kungiyar Hamas. Gwamnatin Moscow dai ta shafe shekaru ta na kokarin daidaita alaka da masu fada a ji a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da Isra'ila da Falasdinu. Amma tun bayan fara yakin Isra'ila a Gaza da kuma mamayar da ita Rashar ta kaddamar a Ukraine, Shugaba Putin ya kara yaukaka dangantaka da Hamas da kuma Iran.

Fadar Kremlin dai ta sha sukar matakin da Isra'ila ta dauka kan harin na watan Oktoba, tare da yin kira da bangarorin su mayar da wukakensu cikin kube.