1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta kai hari kan wata makaranta a Gaza

August 10, 2024

A kalla mutane 100 ne suka mutu yayin da wasu gommai suka jikkata sakamakon hari ta sama da Isra'ila ta kai kan wata makaranta a Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4jJqZ
Isra'ila ta kai hari kan wata makaranta a Gaza
Isra'ila ta kai hari kan wata makaranta a GazaHoto: Omar Al-Qattaa/AFP/Getty Images

Majiyoyin tsaro na Falastinawa da ke Zirin Gaza sun ce, Isra'ila ta kaddamar da harin ne a kan makarantar Al-Tabeen da ke kasancewa mafaka ga 'yan gudun hijira a lokacin da mutane ke tsaka da sallar Asuba.

Dakarun sojin Isra'ila sun ce sun kai harin ne saboda akwai maboyar kwamandojin Hamas a cikin makarantar. Sojojin sun kuma ce sun dauki matakan kaucewa farwa fararen hula, sai dai sun zargi mayakan Hamas da gudanar da ayyukansu daga cikin jama'a.