Isra'ila da Hezbollah sun kai wa junansu hari
February 14, 2024Hukumomin Lebanon sun ce fararen hula uku da wani dan kungiyar Hezbollah sun mutu a wasu jerin hare-hare da Isra'ila ta kaddamar. Rundunar ta ce, harin da Lebanon ta kaddamar ya rutsa da Sajan Omer Sarah Benjo a arewacin Isra'ila. Ta kuma kara da cewa, an kai hare-hare ta sama kan yankunan da mayakan suke a kudancin Lebanon din.
Karin bayani: Fargabar yaki tsakanin Isra'ila da Lebanon
Yayin da babu wanda ya dauki alhakin kai harin rokar, Ana fargaba musayar wuta tsakanin bangarorin biyu ka iya fadada rikici tsakanin Isra'ila da kuma mayakan Hezbolla da ke samun goyon bayan Iran.
Shugaban rundunar sojin Isra'ila, Herzi Halevi ya ce za su zafafa mataki na gaba inda za su yi amfani da dukannin kayan aiki kana su hada karfi da karfe; ya na mai ikrarin kungiyar Hezbolla zata girbi abun da ta shuka. A nashi bangaren, shugaban kungiyar ya yi ikrarin cewa ba za su dakatar da bude wuta daga kudancin Lebanon ba har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Zirin Gaza.