1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Fargabar yaki tsakanin Isra'ila da Lebanon

January 18, 2024

Yanayin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya a kan iyaka tsakanin Isra'ila da Lebanon ya fara janyo wani hali na yaki.

https://p.dw.com/p/4bPvE
ISRAEL-LEBANON-PALESTINIAN-CONFLICT
Hoto: Jalaa Marey/AFP/Getty Images

Yayin da ake ci gaba da samun zaman tankiya tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbullah ta Lebanon mai samun goyon bayan kasar Iran, akwai fargabar cewa rikici yankin Zirin Gaza tsakanin Isra'ila da Hamas zai fantsama zuwa kasar Lebanon da tekun Bahar-Maliya.

 Isra'ila ta harba jirage masu sarrafa kansu tare da musanyen wuta mayakan Hezbullah, kana galibin fararen hula sun tsere daga yankin kan iyakar kasashen.

Tuni 'yan Lebanon suka fara sayen kayan abinci suna tanada domin yuwuwar shiga yaki tsakanin mayakan Hezbullah na Lebanon da ke samun goyon bayan Iran da kuma dakarun Isra'ila.

Libanon | nach Luftangriffen in Naqoura
Hoto: Ali Hashisho/Xinhua/picture alliance

Heiko Wimmen daraktan wani shiri na Lebanon a kungiyar magance rikice-rikice ta duniya ya gani tuni an shiga yanakin yaki tsakanin bangarerorin biyu, kuma gwamnatin Lebanon ba ta da katabus akai:

"Amma  wani abu gwamnatin Lebanon ta yi da wanda ba ta yi ba, ba yi da wani tarisiri anan. Kungiyar Hezbollah take wuya abu yadda taga dama game da rikicin. Ita Hezbollah ta fara shiga rikicin da harin da ta kaddamar ranar 8 ga wtaan Oktoba. Kwana guda bayana harin Hamas na kashe-kashen da ta yi a Isra'ila."

Tun bayan harin da mayakan Hamas na Falasdinu suka kai kan Isra'ila da ya janyo mutuwar fiye da miutane 1,200 tare da garkuwa da wasu mutanen, ita ma kungiyar Hezbullah ta Lebanon mai samun goyon bayan kasar Iran ta dauki matakin taimakon mayakan na Hams wajen kai hare-hare kan Ira'ila ta kan iyaka.

Kelly Petillo wadda take bincike kan Lebanon a bangaren harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai tana ganin tuni rikicin tsakanin Isra'ila da Hamas ya fara famtsama zuwa rikici na yankin baki daya:

Libanon | ausgebranntes Auto von Hisbollah Kommandeur Wissam Tawil
Hoto: Hussein Malla/AP Photo/picture alliance

"Amma wannan abu ne da za a iya samun kuskure, da zai janyo ya gawurta matuka. Zai iya sauya abubuwa zan ce haka. Yana da matukar wuya a samun daidaito lamuran yanayin sakamakon yadda ake samun rikicin na ta'azzara."

Ita dai  kungiyar Hezbullah ta Lebanon tana da gundun 'yan majalisar dokoki a kasar ta Lebanon kuma tana tafiyar da asibitocin taimakon mutane. Duk da haka 'yan kasar suna nuna dari-dari da shiga yaki, ko da yake kungiyar tana da goyon baya tsakanin al'uma kamar yadda wannan matar da ke birnin Beirut fadar gwamnatin kasar ta Lebanon ke cewa:

"Gaba daya babu wanda ya shirya wa yaki. Amma idan haka ya faru za a samu goyon baya mutane. Fuskantar kalubalen yana kara hadin kai. Ita kanta kungiyar Hezbollah ba ta shirya ba, ba ta da kayan abinci da ruwa da gidaje da sauran su."

Lamaru a yankin na  Gabas ta Tsakiya suna iya sauya cikin hanzari sakamakon yakin da ke ci gaba da faruwa tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu da galibin manyan kasashe dunyia suke dauka a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.