Isra'ila ta kai hare-hare a kudancin Labanan
January 10, 2024Dakarun na Isra'ila sun tabbatar da da kai harin ne a sansanin soji da ke Naqoura, bayan harba wasu rokoki da aka yi daga yankin da kuma ya fada cikin Isra'ilar.
A cewar sojojin na Isra'ila dai, sun afka wa mazaunin 'yan ta'adda ne, yayin kuma da ma'aikatar tsaron kasar Labanan ke cewa hare-haren ramuwar gayya daga Isra'ilar a wannan Laraba, sun fada ne kan wasu kauyuka da ke iyakar kasashen biyu.
A wani labarin kuma, Ma'aikatar lafiya da kungiyar Hamas da ke karkashin Hamas a Zirin Gaza, adadin wadanda suka mutu a cikin sa'o'i 24 da suka gabata sakamakon luguden wuta daga Isra'ila sun kai 147.
Tun bayan fara yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas dai, yanzu jami'an fararen hula dubu 23 da 357 suka rasa rayukansu
Adadin kuma wadanda suka jikkata, su ne mutum dubu 59,410.