1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU: Masalaha kan 'yan gudun hijira

Abdullahi Tanko Bala
September 28, 2023

Ministocin cikin gida na kasashen tarayyar Turai sun kudiri aniyar cimma masalaha kan kwararar yan gudun hijira da ke shigowa ta kan teku

https://p.dw.com/p/4WvLl
Daruruwan 'yan gudun hijira a tsibirin Lampedusa
Daruruwan 'yan gudun hijira a tsibirin LampedusaHoto: Ciro Fusco/Ansa/picture alliance

Ministocin cikin gida na kungiyar tarayyar Turai EU na tattauna yadda za a shawo kan kwararar 'yan gudun hijira da ke shigowa ta kan teku a daidai lokacin da wasu mambobin kasashe kamar Italiya da Jamus ke baiyana damuwa game da karuwar kwararar 'yan gudun hijirar.

Fadar gwamnatin Jamus a Berlin ta ce tana da kwarin gwiwa za a farfado da shirin da ya durkushe na rarraba yan gudun hijirar a tsakanin kasashe 27  na tarayyar Turan, da kuma yarjejeniyar da aka cimma da Masar na dakatar da yan gudun hijirar daga tsallakawa tekun Bahar Rum

Kasashen na Turai dai da majalisun dokokin tarayyar Turai sun dade suna tattaunawa tsawon shekaru don cimma matsaya ta yin kwaskwarima na bai daya ga tsarin ba da mafakar siyasa, sai dai tangardar tafiyar da tsarin ya sanya wasu kasashen fusata da lamarin.

Sai dai ministar cikin gida ta Jamus Nancy Faeser ta ce ta yi imani za a cimma masalaha da gwamnatin Jamus za ta amince da ita.