1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta kai makura kan 'yan gudun hijira

September 20, 2023

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bukaci tsaron kan iyakoki da kuma yin adalci wajen rabon daukar nauyin 'yan gudun hijra a tsakanin kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/4Wc5N
Shugaban kasar Jamus  Frank  Walter Steinmeier
Shugaban kasar Jamus Frank Walter SteinmeierHoto: Hannes P. Albert/dpa/picture alliance

Shugaban kasar Jamus Frank Walter Steinmeier ya ce Jamus na fuskantar matsaloli wajen karbar karin 'yan gudun hijira . Ya ce Jamus kamar kasar Italiya ta kai makura inda lamarin ke nema ya fi karfinta.

Karin bayani: Yarjejeniyar EU da Tunisiya kan 'yan gudun hijira

Ya kara da cewa Jamus ta karbi kashi daya cikin kaso uku na dukkan mutanen da suka nemi mafakar siyasa a kasashen Turai a zangon farko na shekarar 2023. Shugaban kasar ta Jamus ya ce kasashen biyu Jamus da Italiya sun dauki gagarumin nauyi a saboda haka ya bukaci yin adalci wajen rabon daukar nauyin yan gudun hijira a tsakanin kasashen Turai.

Steinmeier ya fara ziyarar kwanaki uku a Italiya inda zai gana da shugaban kasar Sergio Mattarella sannan ya ziyarci tsibirin Sicily da ke kudancin kasar ta Italiya.

Hukumomin Italiya dai tuni suka fara tura wasu 'yan gudun hijirar zuwa tsibirin Sicily daga kananan tsibirai na Lampedusa wanda ya cika makil da sabbin yan gudun hijira da ke kwararowa.