1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

EU ta jingine tattaunawa kan mafakar siyasa

September 20, 2023

Majalisar dokokin tarayyar Turai ta sanar da jingine shirinta na tattaunawa da mambobinta game da batun dakatar da bayar da mafakar siyasa.

https://p.dw.com/p/4WcKC
Hoto: Jean-Francois Badias/AP Photo/picture alliance

Kasashen Turan sun gaza cimma matsaya ne kan wannan batu mai matukar sarkakiya, lamarin da ya kara jefa Jamus cikin tsaka mai wuya, wadda a watan Yulin da ya gabata ta nuna rashin amicewarta da matakin.

Jamus din dai ta nuna damuwarta kan yadda za a iya samun jan kafa wajen bai wa masu neman mafakar siyasar kulawar da ta kamata. 

Wakilin Jamus a majalisar dokokin Turan Michael Claus ya bukaci a hanzarta komawa kan teburin tattaunawa don gaggauta cimma matsayar da ta dace a kan batun.