1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Emirates zai ci gaba da jigilar fasinja a Najeriya

Ubale Musa ZUD/SB
September 1, 2022

Kamfanin jiragen sama na Emirates da wasu kamfanonin ketare biyu sun amince su ci gaba da jigilar fasinja zuwa Najeriya bayan wata takaddama da ta sanya kamfanonin barazanar dakatar da ayyukansu.

https://p.dw.com/p/4GJwE
Airbus A380 | Emirates Airlines
Hoto: Daniel Kubirski/picture alliance

Kama daga kamfanin Delta Airlines na kasar Amirka ya zuwa Emirates na Hadaddiyar Daular Larabawa ko bayan South African Airlines na Afirka ta Kudu dai, sannu a hankali kamfunan sufurin sama na kasashen waje dai na barazanar dakatar da ayyukansu a cikin Najeriya bisa rashin kudade na waje da suke da bukata daga cinikin tikiti.

Jirgin Delta Airilnes na Amirka da ke barazanar daina zuwa Najeriya
Jirgin Delta Airilnes na Amirka da ke barazanar daina zuwa NajeriyaHoto: Nicolas Economou/NurPhoto/picture alliance

Sama da dalar Amirka miliyan 600 ne dai kamfunan suka ce sun makale a bankunan Najeriya, lamarin da ya sanya su barazanar tsayar da jigilar fasinja daga ketare zuwa kasar idan dai ba biya musu bukatunsu ba.

Tun da farko kamfanin Emirates dai ya ce tun daga Alhamis din nan zai tsayar da ayyuka a yayin da dan uwansa na Delta ya tsara ficewa cikin watan gobe na Oktoba.To sai dai kuma tun ba a kai ga ko'ina ba kamfunan sun fara lashe amai, inda  Emirates ya sauya taku; tare da janye aniyarsa da kuma sanar da ci gaba a cikin kasuwar sufurin saman Najeriya kasar mai tasiri. Kamfanin ya ce zai ci gaba da aiki daga birnin Lagos da ke zaman kasuwa mafi tasiri a kasar.

Jiragen Emirates a filin jirgin sama na Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa
Jiragen Emirates a filin jirgin sama na Dubai, Hadaddiyar Daular LarabawaHoto: Reuters/A. Mohammad

Kwanga-gaba-kwan-baya da Emirates din ke yi dai tuni ta fusata hukumomin Najeriya. Ministan sufurin saman kasar Hadi Sirika ya ce kamfunan sufurin ketare na da zabin zama cikin kasar ko kuma ficewa.

''Motsi kadan sai ka ji  Emirates ya ce zai daina zuwa Najeriya, duk da muna da bukatarsu, ai ba su kadai ba ne.'' in ji ministan.

Tarrayar Najeriya dai na zaman kasa ta kan gaba a nahiyar Afirka ga batun fasinjoji na sama, inda a bara kadai aka kiyasta sama da mutane miliyan 15  suka hau jirgin sama  walau ciki ko kuma fita zuwa wajen kasar.

Kyaftin Bala Jibril da ke sharhi bisa harkar sufurin sama a Abuja ya ce Najeriyar na da tasirin da kamar wuya kamfanonin ketare su kawar da idanunsu daga gare ta.