1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun Somaliya sun mutu a harin ta'addanci

October 22, 2023

Rahotannin daga Somaliya sun yi nuni da cewa kimanin dakarun sojin kasar 14 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake.

https://p.dw.com/p/4Xrkx
An kai harin bam a Mogadishu
An kai harin bam a MogadishuHoto: Farah Abdi Warsameh/AP Photo/picture alliance

An dai kai harin ne a cikin wata mota a wani sansanin soji da ke kusa da babban birnin kasar Mogadishu. 'Yan sandan sun tabbatar da cewa daga cikin wadanda suka gamu da ajalinsu har da fararen hula biyu kana harin ya lalata gidajen da ke kusa da sansanin. Kungiyar al-Shaab ta dauki alhakin kai hari, sai dai a cewarta dakarun soji 50 ne suka mutu a harin.

Karin bayani: Somaliland: Hare-haren 'yan tawaye ya karu

Sansanin da aka kai harin dai na kasancewa sabo, wanda aka samarwa jami'an tsaron kasar domin yaki da matsalar tsaro. Kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai dai sun shafe tsawon shekaru suna kai hare-hare a Somaliya da ke yankin kahon Afirka.