1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabaab ta kai hari kan kuratan sojoji

November 6, 2022

Rahotanni sun ce maharin ya kunno kai cikin barikin sojin da karfi sosai, inda ya tayar da bom din da ke jikinsa, lamarin da ya jikkata mutane da dama.

https://p.dw.com/p/4J7SG
Somalia I Die ersten Absolventen der türkischen Militärakademie in Somalia
Hoto: Sadak Mohamed/AA/picture alliance

Wani dan kunar bakin wake ya kai mummunan hari a wani sansanin horas da sojoji da ke birnin Mogadishu na Somaliya. Rahotanni sun ce harin na ranar Asabar ya faru ne a barikin Xero Nacnac, inda ake tantance takardun kuratan sojoji da ma shigar da su aikin na soja.

Kungiyar Al-Shabaab mai fada da gwamnatin Somaliya ta sanar da daukar alhakin kai harin da ke zuwa mako guda bayan wasu tagwayen hare-haren kungiyar da suka yi ajalin mutum 116 a kasar.