1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ban ya kashe mutum 35 a Somaliya

Zainab Mohammed Abubakar
January 4, 2023

Wasu bama-bamai da mayakan al Shabaab suka tayar a cikin motoci biyu,ya kashe mutum 15 daura da jikkata wasu masu yawa a gundumar Hiraan da ke tsakiyar Somaliya.

https://p.dw.com/p/4LjSu
Somalia, Mogadischu | Bildungsministerium von zwei Explosionen getroffen
Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP/picture alliance

Wannan dai shi ne harin baya-bayan nan da kungiyar ta al-Shabaab mai alaka da al Qaeda ta kaddamar, tun bayan da dakarun gwamnati da na mayakan kawancen hauloli, suka fara fatattakar tsagerun daga yankunan da suka dade suna rike da su.

Abdullahi Osman da ke zama daya daga cikin wadanda suka taimaka wajen aikin ceto bayan mummunan harin, ya ce akwai wasu gommai da suka jikkata, wasu sun yi muni.

Tuni kafar yada labaran kungiyar ta al-Shabaab, a cikin wata sanarwar ta dauki alhakin harin.