1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da ayyukan jin kai a wasu sassan jihar Borno

April 12, 2021

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan ta a wasu sassan jihar Borno saboda hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a ofishinta da wasu cibiyoyin kungoyoyin da ke gudanar da ayyukan jin kai a Borno.

https://p.dw.com/p/3rtM6
Nigeria Maiduguri | Flucht vor Boko-Haram | Flüchtlingslager
Hoto: Kristin Palitza/dpa/picture alliance

Ranar Asabar da ta gabata ne dai mayakan Boko Haram suka kai hari a Damasak da ke jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya, inda suka kona ofishin Majalisar Dinkin Duniya da na wasu kungiyoyin agaji, abin da ya sa yawancin ma'aikantan jin kai tserewa daga garin.

Karin bayani: Iswap ta kashe mutane 19 a hari a Borno

Wannan ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da harin da ta kai ga dakatar da ayyukanta a wannan yankin saboda tsoron jefa rayukan ma'aikatanta cikin hadari, ganin mayakan na farautar ma'aikatan jin kai a hare-hare da suke kaiwa.

Yara a daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira da ke jihar Borno
Yara a daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira da ke jihar BornoHoto: Ute Grabowsky/Imago Images

A wata sanarwa dauke da sa hannun babban jami'inta Edward Kallon, Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce kona ofosihnta da na wasu kungiyoyin jin kai ciki har da na kasar Norway abin da damuwa da tashin hankali kuma ya haifar da tsaiko a kokarin tallafa wa 'yan gudun hijira.

Matakin ya haifar da damuwa ga ayyukan jin kai da yake neman kara jefa dubban 'yan gudun hijira cikin mawuyacin hali.

Yawancin masu aikin jin kai da suka tsere daga yankunan sun bayyana cewa dole ce ta sa su barin wuraren ayyukansu, duk sun kwana da sanin cewa dubban 'yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali.

Karin bayani: Najeriya: Muhawara ta barke a kan batun tsaro

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan jin kai suka yi gargadin cewa yanzu haka akwai mutane sama da miliyan hudu da ke fuskantar tsananin yunwa a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya da ke fama da kalubalen tsaro.