1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iswap ta kashe mutane 19 a hari a Borno

Binta Aliyu Zurmi MAB
March 13, 2021

Dakarun gwamnati 15 da wasu mayakan sa-ka hudu sun mutu, a kwanton baunar da 'yan ta'adda suka yi wa ayarin motocin sojoji a dajin Gudumbali a jihar Borno da ke yankin Arewa masu gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/3qbDn
Nigeria Soldaten patrouillieren in Tungushe
Hoto: AFP/Str

Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa wasu mambobin ayarin motin soji 13 sun jikkata a wannan harin da ya yi sanadin mutuwar mutune 19. Amma a cikin wata sanarwa da ta fitar,  kungiyar Iswap da ke da alaka da kungiyar Is a yammacin Afirka ta dauki alhakin harin, tana mai cewa ta kashe mambobin ayarin tare da kama fursunan yaki. Kungiyar ta kuma yi ikirarin lalata motocin soji hudu, tare da kwace makamai da alburusai.  Ita dai Kungiyar Iswap ta balle daga kungiyar Boko Haram a shekarar 2016 kuma tana tafka ta'asa a yankin tafkin Chadi.

Sojojin Najeriya sun tafka asara mai yawa a cikin 'yan shekarun nan daga mayakan Iswap.  Majalisar Dinkin Duniya  ta nunar da cewa matsalar tsaro a yankin Arewa maso gabashin Najeriya ta yi sanadin mutuwar kusan mutane 39,000 sannan kusan miliyan biyu sun rasa muhallansu a shekaru 10 na baya-bayannan.