1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An tsawaita tsagaita wuta a Gaza da kwana guda

November 30, 2023

Kasar Qatar babbar mai shiga tsakani a rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas ta tabbatar da cewa an tsawaita yarjejeniyar tsagaita buda wuta a zirin Gaza da kwana guda har i zuwa ranar Juma'a.

https://p.dw.com/p/4ZbWj
An tsawaita tsagaita wuta a Gaza da kwana guda
An tsawaita tsagaita wuta a Gaza da kwana gudaHoto: Alexander Ermochenko/REUTERS

Ministan harkokin wajen kasar Qatar Majed al-Ansari ne ya sanar da wannan labari a cikin wata sanarwa da ya fidda, inda ya ce an cimma wannan matsaya ne tare da tsoma bakin kasashen Amurka da kuma Masar.

Karin bayani: Gaza: Fatan tsagaita wuta na din-din-din

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin cikar wa'adin yarjejeniyar kwanaki shida da bangarorin da ke gwabza fada suka cimma wanda ya kawo karshe da asubahin ranar Alhamis (30.11.2023).

Karin bayani:  Kokarin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Tuni ma dai kungiyar Hamas da kasashen Yamma ciki har da Amurka da Jamus suka ayyana a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, ta tabbatar da wannan labari na tsawaita wa'adin yarjejeniyar wacce ke ke ba da damar isar da kayan agaji a zirin Gaza.

A daya gefe kuma sakataren Harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Isra'ila inda yake ganawa da firaminista Benjamin Netanyahu kan rikicin da ya barke tun a ranar bakwai ga watan Oktoban da ya gabata.