1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace dalibai a Najeriya

Abdourahamane Hassane
October 10, 2023

'Yan bindiga sun sace dalibai hudu na jami'ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi a arewa maso gabashin Najeriya .

https://p.dw.com/p/4XN3a
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Nasarawa Rahman Nansel ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya bayyana wa manema labarai a garin Lafiya. Inda ya ce yan bindigar sun shiga unguwar dauke da manyan  bindigogi, suka sace daliban uku mata daya namiji. Rundunar 'yan sandan Jihar Nasarawa dai ta tabbatar da cewar ta baza jami'anta zuwa wurare dabam-dabam da nufin gano inda 'yan bindigar suka  shiga da daliban.