1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala zaben gwamnoni a jihohi uku na Najeriya

November 12, 2023

Tashe-tashen hankula da zargin magudi sun mamaye zaben gwamnoni da aka gudanar a jihohi uku na Tarayyar Najeriya da suka hadar da Bayelsa da Kogi da kuma Imo.

https://p.dw.com/p/4YiK4
Nigeria | Präsidentschafts- und Parlamentswahlen
Hoto: Patrick Meinhardt/AFP

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta sanar da cewa an yi garkuwa da daya daga cikin jami'anta, yayin da kungiyoyi da ke sa ido kan zaben suka ba da rahoton harbe mutane biyu ciki har da wani mutum da yi kokarin sace akwatin zabe.

Karin bayani:  Sake zaben gwamna a Jihar Imo 

An dai gudanar da zaben cikin tsauraren matakan tsaro ciki har da hana tafiye-tafiye, sannan kuma rundunar 'yan sanda kasar ta yi amfani da kayan aiki masu yawa don tabbatar a lokacin kada kuri'a ciki har da jirage masu saukar angulu.

Karin bayani:  INEC za ta gurfanar da wadanda suka saci akwati

An fara kidayar kuru'un tun a maraican Asabar (11.11.2023) bayan rufe rufunan zabe, kuma tuni aka fara fitar da kwarya-kwaryar sakamakon zaben wanda hukumar INEC ta ce ta gyara kura-kuren da aka samu a zabukan baya don tabbatar da gaskiya da adalci.