1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen INEC gabanin zaben gwamnoni

March 7, 2023

Kasa da tsawon mako guda da kama hanyar kotu domin kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa da ya shude, kace-nace ya barke a tsakanin manyan jam'iyyun adawar kasar da hukumar INEC.

https://p.dw.com/p/4OMuG
Najeriya | Sakamakon Zabe | Mahmood Yakubu | INEC
Mahmood Yakubu shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Najeriya INEC Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Manyan jam'iyyun adawar Najeriya dai na shirin yi wa na'urar BVAS kallon tsaf, yayin da Hukumar Zabe ma Zaman Kanta ta Kasar INEC ke fadin babu lokaci a halin yanzu. Tun a karshen mako ne dai kotun sharia'ar zaben ta bai wa jam'iyyun PDP da Labour damar nazarin daukacin kayan zaben, domin neman hujjar ikirarin magudin da suke yi a kan zaben. Kafin hukumar INEC ta gabatar da sabuwar bukatar da a cikinta take fadin babu lokaci na binciken na'urar BVAS da hukumar ta ce tana bukatar sake fasalinta, domin kai wa ya zuwa zaben gwamnonin da ke shirin ya gudana a karshen mako. BVAS din dai ce ya zuwa yanzu ke zaman  babban fata a bangaren masu adawar da suka dauki lokaci suna ihun kura a duhu, yanzu haka kuma ke da jan aikin gamsar da alkalan kotun jerin korafin da suke yi kan zaben. Kuma babban tsoro a zuciya ta adawar dai na zaman jirkita hujja a cikin kokarin sake fasalin a bangaren hukumar da ake yi wa zargin hada kai da masu mulkin kasar, a kokarin cika burin son rai.

Najeriya | Zabe | 2023 | INEC | Na'ura
Na'urar tantance masu zabe a Najeriya BVASHoto: Benson Ibeabuchi/AFP

Kwamared Sa'idu Bello dai na zaman jigon jam'iyyar PDP kuma ya ce, ba hujjar dorawa zuwa gaba cikin tsarin da ginshikinsa ke da raunin gaske. To sai dai kuma in har 'yan lemar suna fadin da sauran sake, ga hukumar zaben ta INEC duk wani kokari na jinkiri ga bukatar sauyin fasalin na iya shafar zaben gwamnonin da ke shirin ya gudana 'yan kwanaki kalilan da ke tafe. Tuni dai INEC din ta nemi kotun shari'ar da ta sauya lokacin yin nazarin domin samun damar iya sauyin fasalin da ke da tasirin gaske, ga kokarin kyautata tsarin zaben da ke shan suka cikin kasar a halin yanzu. Barristaer saidu Mohammed Tudun wada dai na zaman wani lauya mai zaman kansa a Najeriyar da kuma ya ce, kotun zaben na da karfin tabbatar da adalci a cikin kace-nacen da ke iya kara jefa daukacin kasar cikin rudani. Rawar hukumar ta INEC zuwa gaba dai na da tasirin gaske, ga makomar dimukuradiyyar kasar da ke cikin wani yanayi yanzu haka. Ali M Ali dai na zaman daya a cikin kakakin yakin neman zabne jam'iyyar APC, kuma a cewarsa ba hujjar hana hukumar zaben kai wa ya zuwa sauke babban nauyin da ke bisa kanta.