1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zirga-zirgar jirage cikin gari a Lagos

July 30, 2024

A Jihar Lagos an fara gwajin jirgin da zai fara shiga sassan wurare da nufin kakkabe tsoffin dabaru na sifuri domin tafiya da zamani

https://p.dw.com/p/4ivAS
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

 Ba tun yau bagomnatin Gov Babajide sanwo olu take ikirarin tabbatar da gyara hanyoyin sufuri a fadijn jihar kama daga tituna da ta ruwa inda ake samun jiragen kwale-kwale na zamani.To sai dai a wannan karon gwamnatin Lagos  ta fito da tsari na samar da zirga-zirgar jiragen cikin gari.

Nigeria Rigasa | Polizist am Bahnhof an der Abuja-Kaduna Zugstrecke
Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

To sai dai hanzari ba gudu ba mai ba wa gomna shawara ta fannin sufuri a Jihar ta lagos Mr Showa Giwa ya ce wajibi ne wasu sasasan jihar a daina amfani da adaidaita sahu. A yanzu haka dai kamar yarda kwamishinan sufuri na jihar mr Oluwaseun Osiyemi ya ce zaa fara sinturi ne na gwaji ga jIragen na cikin Gari kafin a fara gadan-gadan.