1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka da Burtaniya sun yi gargadi kan Najeriya

Abdullahi Tanko Bala
July 29, 2024

Amurka da Burtaniya da Kanada sun yi gargadi kan Najeriya gabanin zanga zangar da ake shirin gudanarwa a kasar kan wahalhalun tattalin arziki da tsadar rayuwa.

https://p.dw.com/p/4isbo
Fargaba kan zanga zanga a Najeriya
Fargaba kan zanga zanga a NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture alliance

Ma'aikatar harkokin wajen Burtaniya ta ce akwai barazanar tashin hankali daga 29 ga watan Yuli zuwa 10 ga watan Augusta, ta na mai nuni da cewa jerin zanga zangar da aka yi a baya sun rikide zuwa tashin hankali.

Gwamnatin Kanada ita ma ta yi gargadin cewa zanga zangar na iya rinchabewa a kowane lokaci.

A halin da ake ciki kuma ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya shawarci Amurkawa su kauce wa wuraren tarukan jama'a da wuraren zanga zanga.

Najeriya na fuskantar tsadar rayuwa mafi muni da aka dade ba a gani ba a tsawon lokaci.

A watan Yunin da ya gabata tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki ya kai kashi 34.2 cikin dari yayin da farashin abinci ya tashi da fiye da kashi 40 cikin dari a cewar alkaluman hukumar kididdiga ta Najeriya.