1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Agaji ya fara isa yankin Zirin Gaza

October 21, 2023

Kimanin manyan motocin dakon kaya guda 20 dauke da kayan agaji suka isa zirin Gaza da rikici ya daidaita ta mashigin iyakar Rafa da ke tsakanin Gaza da kuma Masar.

https://p.dw.com/p/4XrAg
Hoto: Omar Aziz/AP Photo/picture alliance

Wannan dai shi ne karon farkon da aka isarda kayan agaji zuwa Gaza tun bayan fara rikici tsakanin Isra'ila da kuma kungiyar Hamas fiye da makwanni biyu da suka gabata. Mashigin iyakar Rafa na kasance hanya daya tilo zuwa Gazaba baya karkashin ikon Isra'ila, inda aka amince da shigar da agaji daga Masar bayan da Amirka da ke dasawa da ita ta bukaci yin hakan. Shugaban kula da ayyukan jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths ya yi gargadin cewa, kada rukunin farko na kayan agajin ya kasance na karshe. Dama dai an dauki tsawon kwanaki, jiragen sama da kuma motocin dakon kaya na kai kayan agaji zuwa iyakar ta Rafa, sai dai ba su sami damar isar da su zuwa Gaza ba.Neman mafita a rikicin Isra'ila da Hamas