1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Masar na taron zaman lafiya kan rikicin Gaza

October 21, 2023

Shugabannin kasashen duniya za su hallara a kasar Masar domin gudanar taro kan rikicin Isra'ila da Hamas, yayin da ake fargabar bazuwar rikicin a yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/4XqCy
Ministan harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock da takwaranta na Masar, Samih Shoukry.
Ministan harkokin wajen Jamus, Annalena Baerbock da takwaranta na Masar, Samih Shoukry.Hoto: Ahmed Hasan/AFP

A makon da ya gabata ne dai kasar Masar ta kira taron domin shawo kan rikici da kuma sanin makomar Falasdinawa.

Ministan harkokin wajen Masar, Sameh Shoukry ya ce taron zai mayar da hankali ne wajen ganin an tsagaita bude wuta da kuma kai kayayyakin agaji zuwa zirin Gaza.

Karin bayani: Chaina za ta hada hannu da Rasha don magance rikicin Gaza

Kasar Masar da ta shirya taron, kana kasar Larabawa ta farko da ta sanya hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila a shekarar 1979 ta damu matuka kan yadda jama'a a zirin Gaza za su kaura zuwa yankinta.

Karin bayani: Masar: Adawa da kwararar 'yan gudun hijira 

Kafafen yada labaran kasar Masar sun ruwaito cewa daga cikin wadanda za su halarci taron har da shugaban Faladinawa Mahmoud Abbas da takwarorinsa na Jordan da kuma Italiya da ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres.