1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta kashe mutane a Najeriya

August 27, 2024

Gomman mutane ne hukumomi ke tabbatar da cewa sun salwanta a Najeriya, sakamakon ta'adin da ambaliyar ruwa ta yi a 'yan kawanakin nan a yankin arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4jx7t
Ambaliyar ruwa a Najeriya
Ambaliyar ruwa a NajeriyaHoto: Reed Joshu/AP/picture alliance

Akalla rayukan mutane 49 ne hukumomi a Najeriya ke tabbatar da cewa suka salwanta, sakamakon ta'adin da ambaliyar ruwa ta yi a 'yan kawanakin nan a yankin arewacin kasar.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar NEMA, ta ce ruwan sama mai karfi da aka yi ta yi a 'yan tsakanin nan, har ila yau ya yi sanadin raba mutane dubu 41, 344 da muahllansu.

Matsalar kuwa ta shafi jihohin Adamawa ne da Jigawa da kuma jihar Taraba.

Ibtila'i ne da ake gani a kusan kowace shekara a kasar, inda ko a shekarar 2022 ma ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 600 a Najeriyar, kuma wasu kimanin miliyan guda da dubu 400 suka rasa gidaje.

Hukumar ta NEMA, ta kuma nuna cewa a yanzu ne ake shiga kololuwar lokacin samun mamakon ruwan sama a daminar bana.

Ambaliyar da ke shafar gonaki masu yawa, na zuwa ne yayin da tsadar rayuwa ke kara kamari a Najeriyar, inda kayan abinci ke tsananin tsada ga marasa karfi.