1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'iNajeriya

Najeriya: Ambaliya ta janyo asarar rayuka

August 14, 2024

Mamakon ruwan sama da aka yi ya haifar da ambaliyar ruwa a kanana hukumomi 17 da ke jihohin Borno da Yobe, inda ya lalata dubban gidaje da makarantu da kasuwanni da kuma Gonaki.

https://p.dw.com/p/4jTMU
Najeriya | Ambaliya | Borno | Yobe | Bauchi
Bala'in ambaliyar ruwa, na barazana a NajeriyaHoto: Muhammad Bello Ibrahim/DW

Tuni dai gwamnatocin jihohin na Yobe da Borno, suka dauki matakin kai dauki ga wadanda bala'in amlabiyar ruwan ta shafa. Jihohin Arewa maso  gabashin Najeriya na shaida ganin ibtila'in ambaliyar ruwa a wannan lokaci, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi tare da gurgunta harkokin sufuri da noma da ma kasuwanci. Manyan hanyoyi da su ka hada shiyyar da sauran sassan Najeriyar kamar muhimmiyar hanyar da ta hada jihohin Borno da Yobe da Bauchi da bangaren jihohin Arewa maso Yammacinkasar, ta yanke saboda ambaliyar da aka yi a wani yanki na jihar Bauchi.

Yanzu haka a jihar Yobe bayan lalata gidaje ambaliyar ta kuma lalata gonaki tare da lalata hanyoyi, abin da ya sa al'ummomi da dama suka kauracewa matsugunansu zuwa wuraren da hukumomi suka samar ga mutane. Haka wannna matsala take a jihar Borno, inda nan ma aka samu rubtawar gidaje da lalacewar gonaki saboda matsalar ta ambaliya. Ana dai bayyana fargabar barkewar cututtuka, sakamakon wannan ibtila'i. Sai dai hukumomi na cewa suna bakin kokarinsu, domin taimakon wadanda ambaliyar ta shafa. Masu yaki da gurbatar muhammali na kira ga hukumomi su karfafa aikin fadakar da al'umma kan hadarin lalata muhammali, wanda shi ne ke haifar da irin wannan abaliyar ruwan ko za a samu saukin matsalar a nan gaba.