1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A a Aljeriya Bouteflika ya yada kwallon mangwaro.

Abdourahamane Hassane
April 4, 2019

Bayan kwashe sama da shekaru 30 yana mulki Abdelaziz Bouteflika ya dangana ya sauka daga karagar mulkki, amma dai sai da aka yi ta kai ruwa rana a zanga-zangar da al'umma ta rika yi domin tilasta masa da ya yi marabus.

https://p.dw.com/p/3GDcZ
Algerien Präsident Abdelaziz Bouteflika
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Djarboub

 Abdelaziz Bouteflika wanda aka haifa a ranar 02 ga watan Maris na shekara 1937 kimanin shekaru 82 ya zo ne a kan karagar mulkin Aljeriya tun a shekara ta 1999. Sai dai a sahekarun baya-baya nan, ya yi ta fama da rashin lafiya mutuwar rabin jiki, abin da ya sa al'umma ta rika yin borai domin ganin ya sauka daga mulkin saboda kasawa. Kafin a ranar biyu ga watan Afrilu na shekara ta 2019 sojoji su tilasta masa yin marabus.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna