1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Likitoci sun shirya gangamin a Aljeriya

Yusuf Bala Nayaya
March 18, 2019

Kungiyar likitocin masu zaman kansu ta (CAMRA) ta yi wannan shela a wannan Litinin. Ta kuma yi kira ga dalibai da ke koyon aikin likita a kasar su bi sahun jami'an lafiyar.

https://p.dw.com/p/3FFyO
Algerien Proteste in Algier
Hoto: Reuters/R. Boudina

Likitoci a kasar Ajeriya sun yi kira na a gudanar da babban gangami na adawa da gwamnatin Abdelaziz Bouteflika lokacin da za a yi bikin ranar tuni da lokacin da kasar ta samu 'yancin kanta. Bikin da za a yi a ranar Talata. Matakin da ke kara nuni na matsin lamba kan shugaban kasar da ke fama da matsala ta rashin lafiya.

Kungiyar likitocin masu zaman kansu ta (CAMRA) ta yi wannan shela a wannan Litinin. Ta kuma yi kira ga dalibai da ke koyon aikin likita a kasar su bi sahun jami'an lafiyar a wannan gangami me kudiri na ganin bayan kaka gidan wasu da ke kan karagar mulki a kasar tsawon lokaci.

Shugaban na Aljeriya dai ya kwashe shekaru 20 a kan karagar mulki. A makon da ya gabata ya ajiye aniyarsa ta karin neman wa'adi a karo na biyar sai dai batu na sauka daga kujerar mulki bai taso ba.