1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shuga Bouteflika ya bayyana matakin kauracewa shiga takara

Abdoulaye Mamane Amadou
March 11, 2019

Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya fice daga jerin 'yan takarar shugaban kasa makwanni biyu bayan zazzafar zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/3Eooj
Algerien | Abdelaziz Bouteflika
Hoto: imago/photothek/T. Trutschel

Shugaban Aljeriya da ya gana da shugaban hafsan sojan kasar baqyan ya isa gida a ranar Lahadi 10.03.2019 inda bayyana shirya wani taron da zai kai ga duba hanyoyin kawo gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar domin samar da wani sabon kundin tsarin mulki a wannan shekara. Kana shugaban ya ce ba zai tsaya takarar shugabancin kasa ba  yana mai cewa ba ya bukatar wani wa'adi na biyar na mulki duba da yanayin shekaru da kuma rashin lafiya.

Sai dai shugaban ya ce za a dage zaben kasar na shugaban kasa da ake shirin gudanarwa a ranar 18 ga watan gobe har izuwa gabanin babban taron da zai tattara daukacin bangarorin tafiyar siyasar kasar.

Birnin Algers da sauran yankunan kasar sun barke da sowa da hayaniyar motoci bisa jin matakin na Shugaba Abdelaziz Bouteflika wanda ke cika shekarunsa na 20 kenan a kan madafan iko kuma ke fuskantar matsin lanba daga yan kasar da ke cewar ko kadan ba za su lamunta shugaban ya sake tsaywa takara ba saboda rashin lafiya.