1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

'Yan bindiga a jihar Filato sun kashe gomman mutane.

December 26, 2023

Bayanai daga Najeriya na cewa adadin rayukan mutanen da suka salwanta a jerin hare-haren da 'yan bindiga suka kai kan wasu yankuna a jihar Filato ya kai akalla mutum 160.

https://p.dw.com/p/4aa1g
Hoto: AFP/Getty Images

Hare-hare ne da suka faro daga Bokkos da yammacin ranar Lahadi, suka shige cikin yankin Barikin Ladi, inda da farko aka bayar da labarin mutuwar mutum 113.

Akwai ma wasu sama da mutum 300 da maharan suka jikkata, mutanen da a halin yanzu aka kwantar a asibitocin yankin Bokkos.

Hukumomin yankin na Bokkos dai sun ce hare-haren sun shafi akalla kauyuka 20 da ke cikin kananan hukumomin biyu na Bokkos da kuma Barikin Ladi

Wani dan majalisar jiha Dickson Chollom, wanda ya nuna takaici da abin da ya faru, ya yi kiran jami'an tsaro da su dauki mataki na gaggawa.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da rashin daukar matakan da za su kawo karshen kare-kashe da ake yi a yankunan karkara a jihar Filato.