Daliban marasa karfi a jami'o'in gwamnatin tarayya a Najeriya na fuskantar cikas a karatunsu, bayan da hukumomi da dama sun kara kudin makaranta da kashi 100. Wananan mataki ya tilasta wa wasu dalibai marasa galihu barin makaranta, wasu kuma na iya jinkirta karatunsu na akalla shekara guda. Ya za a magance wannan matsala?