1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Zargin 'yan sanda da cin-zarafi

Uwais Abubakar Idris LM
November 28, 2024

Kungiyara Kare Hakkin dan Adam ta Kasa da Kasa Amnesty International, ta kadammar da rahoton binciken da ya gano zargin yadda 'yan sanda da cin-zarafi a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka yi a Najeriya.

https://p.dw.com/p/4nXVV
Najeriya | Lagos | Zanga-zanga | Tsadar Rayuwa | Amnesty International | 'Yan Sanda
Amnesty International ta zargi 'yan sanda da murkushe masu zanga-zanga a NajeriyaHoto: Fawaz Oyedeji/AFP/Getty Images

Bincike ne mai zurfi kungiyar ta ta yi a kan abin da ya faru, a lokacin da matasan Najeriyar suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa ta tsawon kwanaki 10 a watan Augustan da ya gabata. Amnesty ta ce ta tattara bayanai daga shaidu na gani da ido da ma abin da jami'anta suka shaidar a kan yadda 'yan sandan Najeriyar suka yi amfani da karfin da ya wuce iyaka a kan masu zanga zangar a jihohi shida na kasar da Abuja. Matasan dai sun ta artabu da 'yan sanda a kan zanga-zangar da suka yi ta nuna koken cewa rayuwa ta yi masu tsada, musamman a jihohin da suka hadar da Kaduna da Kano da Jigawa da Borno da ma babban birnin tarayya Abuja.

Abuja: Yaran da aka saka bayan tsare su

Matasan da suka shiga zanga-zangar sun yi ta koken abubuwan da suka faru, Kwamared Yahya Abdullahi na cikin matasan da suka shiga zanga-zangar a wancan lokaci, ya mayar da martani a kan rahoton na kungiyar Amnesty International din. Duk da shidun da kungiyar ta Amnesty International ta bayyana da ta bankado a rahoton nata da ya shaidar da kame mutane 1,200 ciki har da mata da yara kanana, rundunar 'yan sandan Najeriya ta yi ta musanta cewa ta yi amfani da karfi a kan masu zanga-zangar tare da cewa jami'anta ma aka jikkata. Binciken na Amnesty International ya sake tono abubuwa da dama  da kungiyoyin farar hula ke rajin lallai sai gwamnati ta dauki mataki a kai, inda bayan sakin wasu daga cikin wadanda aka kama akwai batun biyan diyya ga 'yan uwansu da gwamnati ta yi shiru a kai.