1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafatawa mai zafi a zaben Osun

Abdoulaye Mamane Amadou
July 16, 2022

A Najeriya fafatawa na kara tsanani tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da babbar jam'iyyar adawa ta PDP, a zaben gwamnan jihar Osun da ake gudanarwa a Kudu maso Yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/4EEkE
Nigeria Regionalwahlen 2019
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Ya zuwa yanzu komai na tafiya daidai a zaben gwamnan jihar Osun da ke yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. Wakilin DW Mansur Bala Bello ya ce "Zaben na tafiya a cikin tsanaki da kwanciyar hankali, sai dai ana zargin amfani da kudi ya mamaye bakunan 'yan siyasa."

Rahotanni sun ce ana kan-kan-kan, tsakanin jam'iyyar APC mai mulki da babbar jam'iyyar adawa PDP. Tun da fari dai Hukumar Zaben Najeriya mai Zaman Kanta INEC, ta ce ta isar da komai a kan lokaci kafin a bude runfunan zaben. Ana dai hasashen fiye da mutane miliyan daya da dubu 500 ne za su fito domin zabar sabon gwamna, a zaben da ke zaman zakaran gwajin dafi ga babban zaben Najeriya na 2023 da ke tafe cikin kasa da watanni bakwai masu zuwa. Hukumomin tsaron kasar dai sun tanadi matakan tsaro, a wani mataki na hana barkwewar rikici.