1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mutane da dama sun yi zaben Jamhuriyar Nijar

Gazali Abdou Tasawa SB
December 27, 2020

An fara samun zargin magudi tsakanin masu mulki da 'yan adawa na Jamhuriyar Nijar. Mutane sun yi tururuwa wajen kada kuri'a a zaben.

https://p.dw.com/p/3nGOP
Zentralafrikanische Republik | Wahlen 2020 | Wahllokal in Bangui
Hoto: Jeff Murphy Barès/DW

Zaben shugaban kasa  da na ‘yan majalisar dokoki da ya gudana a wannan Lahadi a Jamhuriyar Nijar inda jama’a da dama suka shaida cewa mutane sun fito dafifi a yankuna na kasar domin zaben wanda amma ‘yan adawa da masu mulki kowa na zargin dan uwansa da aikata sata a cikin zaben, abin da aka saba gani tsakanin   'yan siyasa.

Zentralafrikanische Republik | Wahlen 2020 | Wahllokal in Bangui
Hoto: Jeff Murphy Barès/DW

A hakumance ya zuwa yanzu hukumar zabe ba ta bayyana alkalumma na adadin mutanen da suka fito zaben na wannan karo ba, a Zahiri take cewa a yankunan da dama jama'a sun fito dafifi domin kada kuri’ar tasu, kuma jam’iyyun siyasa sun dauki mataki na kasawa da tsarewa a runfunan zaben kamar dai yadda za ku ji a firar da ta hada ni da wakillan jam’iyyun siyasa a wata runfar zabe da na ziyarta a birnin Yamai.

Shugabannin runfunan zabe da dama a birnin Yamai dai sun tabbatar da cewa har ya zuwa yammacin Lahadi zaben ya wakana a cikin kwanciyar hankali kamar dai yadda daya daga cikinsu ya tabbatar mani.

Karin Bayani: Ana ci gaba da zaben Jamhuriyar Nijar

Sai dai duk da yadda a runfunna zabe da daman a birnin Yamai al’amurra suka dunga tafiya salin alin ‘yan adawa da masu mulki sun yi ta zargin junansu da aikata sata ko yunkurin yin hakan a cikin zaben nay au kamar dai yadda za ku ji daga bakin wasu magoya bayan adawa da na masu mulki da na yi kicibis da su bayan kada kuri’arsu a birnin na Yamai.

Zentralafrikanische Republik | Wahlen 2020 | Wahllokal in Bangui
Hoto: Jeff Murphy Barès/DW

Da misalin karfe takwas ta daren wannan Lahadi ne dai ya kamata a rufe runfunan zabe a fadin kasar Nijar. Sai dai domin shawo kan matsalar jinkirin da ake samu wajen bude runfunan zabe a bisa wasu dalillai  a wasu yankunan kasar wata doka ta hukumar zabe ta tanadi cewa ko ma a wani lokacin runfar zabe ta bude to ya zamo dole a gare ta ta kwashe awoyi 11 tana aiki Tun a daren wannan Lahadi ne dai  ne dai hukumar zabe mai zaman kanta z ata soma kwanan zaune na soma tattarar sakamakon zaben na wucin gadi wanda ake sa ran hukumar zaben ta bayyana shi a cikin kwanaki biyar masu zuwa ga kotun tsarin mulkin wacce ita kuma za ta bayyana kammalallen sakamakon a cikin makonni biyu masu zuwa.