1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Masu zabe a Jamhuriyar Nijar na kada kuri'a

Salissou Boukari SB
December 27, 2020

Dubban mutane na ci gaba da tururuwa domin kada kuri'a a zaben Jamhuriyar Nijar wanda ke zama karo na farko da gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga watan gwamnatin ta farar hula.

https://p.dw.com/p/3nG2n
Niger Niamey | Wahlen
Hoto: Issouf SANOGO/AFP

A Jamhuriyar Nijar ana kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa zagaye na farko gami da na 'yan majalisar dokoki na kasa. Tun dai da musalin karfe takwasne akasarin run funan zaben suka buda, sai dai a runfa mai lamba 00 da 01 inda shugaban kasa da mambobin gwamnati ke zabe, an soma zaben ne wajejen karfe 10 da kusan rabi inda shugaban kasa Issoufou mahamadou tare da mai dakinsa suka kada kuri'a.

Niger Niamey | Wahlen
Hoto: Issouf SANOGO/AFP

Wannan rana dai ta 27 ga watan Disamba, ta kasance rana mai cikeken tarihi da al'ummar kasar Nijar da kuma shugaban kasa Issoufou Mahamadou wanda bayan da ya yi zabe a runfa mai lamba 00 da 01 ya yi bayabayani ga manema labarai inda ya ce wannan shine karo na farko a cikin shekarau talatin da akae zaben shugaban kasa ba tare da ya na dan takara ba:

Ya ce: "Mako biyu da suka gabata mun shirya zaben kananan hukumomi, kuma yanzu ga shi muna na shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, don haka wannan babban rana ce a gare ni da kuma 'yan Nijar baki daya da a karon farko wani shugaban kasa da aka zaba ya kammala na shi mulki zai damka wa wani sabon shugaban kasa da za a zaba. Ina fatan kuma hakan shi ne abun da ake jira wanda zai kai mu da kara karfafa dimukuradiyyar kasarmu Jamhuriyar Nijar."

Karin Bayani: Hukumar CSC ta gana da 'yan siyasa

A wannan runfa da shugaban kasa Issoufou Mahamadou ya yi zabe, nan ne kuma dan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya mai mulki Bazoum Mohamed ya yi zabe inda bayan ya kammala ya ce ya yaba yadda aka tsara wannan zabe:

Daga na shi bangare dan takarar neman shugabancin kasar ta Nijar a karkashin inuwar jam'iyyar ANDP Zaman lafiya Alhaji Moussa Baraze da shi ya yi zaben a mahaifarsa ta Dosso da ke a nisan km 130 da Yamai babban birnin kasar ta Jamhuriyar Nijar.

Niger Tillabéri | Wahlen
Hoto: Marou I. Madougou/DW

An fdai samu tawaga-tawaga ta yan kallo masu tarin yawa kama da gay an kallon na nan gida Nijar, da kuma na kasashen waje irin na Tarayyar Afirka, ECOWAS, CEN SAD da dai sauransu, kuma shugaban hukumar zaben Najeriya Mahamadu Yakubu, na daga cikin wadanda suka zo domin ganin yadda zaben na Nijar zai gudana. Said ai ya ce idan har aka kiyaye tsari na sakamako tun na runfar zabe a bi shi har ya zuwa koli to babu wani zancan a ce an yi magudin zabe.

Karin Bayani: Kotun kolin Nijar ta ja kunnen 'yan siyasa

An dai samu cinkoson zaben wanda aka dade ba'a ga irinsa ba, abun da ke nuni da cewa mutane na da babban buri ga wannan zabe. Kuma yayin da na je mazabu na makarantar Kouado da ke unguwar Tallage na yi kallon dan mutun inda kowa ke fatan ganin ya yi zaben. Ga baki daya dai za a ce hukumar zabe CENI na da kimanin kwanaki biyar na ta mika sakamakon zaben da ta tattara na wuccin gadi domin mika su ga Kotun tsarin mulki da z ata bada sakamako na dindin cikin makonni biyu. Za a dai rufe runfunan zaben awoyi 11 bayan da aka buda runfar zabe.