1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben gwamnoni a jihohi 28 cikin 36 na Najeriya

March 18, 2023

A wannan Asabar al'umma a Najeriya sun fita rumfunan zabe domin kada kuru'a a zaben gwamnoni da kuma 'yan majalisun dokokin jihohin a jihohi 28 cikin 36 na kasar.

https://p.dw.com/p/4OsEl
Nigeria | Schlange bei der Präsidentschaftswahl
Hoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Jama'a da dama sun zura ido kan zaben jihar Adamawa da ke shiiyar arewa maso gabashin kasar, inda ake da 'yar takara mace wadda idan ta samu nasara za ta kasance mace ta farko a Najeriya da za ta ja ragamar jiha a kasar.

Masu sanya ido kan zabe na kungiyoyin kasa da kasa dai sun bayyana cewa an samu tarin matsaloli a zaben shugaban kasa da kuma na 'yan majalisun tarayyar da ya gabata, hakan ya sa ake ganin za a kara zuba ido ga hukumar zaben mai zaman kanta ta kasar INEC, wadda ta dage zaben gwamnonin da aka tsara gudanarwa makon da ya gabata domin daidaita na'urar zabe ta BVAS.

Rahotanni sun baiyana yadda aka tsaurara matakan tsaro domin yi wa tufkar hanci musamman a jihohin Kano da ke arewacin kasar da kuma Rivers da ke kudanci, inda nan ne aka fuskanci rikicin bayan zabe a watan da ya gabata.