1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Fafatawa tsakanin Haley da Trump

Abdourahamane Hassane
January 23, 2024

Ana gudanar da zaben fisdda gwani na ‘yan jam'iyyar Republican a Jihar New Hampshire,da ke a arewa maso gabashin Amirka.

https://p.dw.com/p/4bbOA
Donald Trump und Nikki Haley
Donald Trump und Nikki HaleyHoto: Jonathan Ernst/REUTERS

 A hasashe da kafofi masu zaman kansu suka bayyana,Trump dan shekaru 77  ya na gaban Nikki Haley  'yar shekaru 52 da kusan maki 30 a zaben fidda gwanin. Masu aiko da rahotanni na cewar Janyewar da gwamnan jihar Florida Ron DeSantis ya yi a karshen makon jiya, wanda ake ganin a matsayin  babban abokin hamayyar  Donald Trump kana tsohon na hannun damansa. Za ta bude hanya ga Trump din wajen samun nasarar tsayawa takara a zaben shugaban kasa na Amirkan da za a yi a ranar biyar ga watan Novemba na wannan shekara  inda zai kara da dan takarar jam'iyyar demokrat   Joe Biden

.