1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarima Harry ya garzaya kotu kan janye masa tsaro

Abdul-raheem Hassan
December 5, 2023

Lauyoyin Yarima Harry sun shiga kotu don kalubalantar janye masa tsaro da masarautar ta yi tun bayan da ya ajiye sarauta don fara sabuwar rayuwa da iyalinsa a arewacin Amirka.

https://p.dw.com/p/4Zoyk
YArima HarryHoto: Victoria Jones/REUTERS

Shari'ar game da rasa kariya ta musamman ita ce ta baya-bayan nan a cikin jerin kararrakin kotu da Harry ya fara, tun abyan tabbatar wa mahaifinsa Sarki Charles na III sarautar Birtaniya.

Harry yana daukar matakin shari'a a kan ma'aikatar harkokin cikin gida ta Burtaniya kan shawarar da wani kwamiti da ke kula da tsaron fadar masarautar Buckingham ta yanke a watan Fabrairun 2020 na rashin samun damar da yake da ita a baya.

Za a gudanar da shari'ar ta baya-bayan nan a cikin sirri, ba tare da 'yan jarida ko jama'a sun san me ake ciki ba, saboda shaidar sirri kan matakan tsaro. A ranar Alhamis ne za a kammala sauraren karar, inda a nan gaba za a yanke hukunci.