Ajantina zabe tattare da matsalar tattalin arziki
October 20, 2023Talla
Shugaba mai barin gado Alberto Fernández,da mataimakiyarsa Cristina Fernández su dukkaninsu ba za su tsaya takara ba. Dan takarar jam'iyyar masu ra'ayin kyamar baki wanda ake ganin yana da sassaucin ra'ayi,Javier MileIwanda ake hasashen zai iya taka rawar gani a zaben,. zai fafata da Sergio Massa, na kawancen jam'iyyar Peronist da Patricia Bullrich, shugabar 'yan adawa ta jam'iyyar masu ra'ayin jari hujja. Ajantina na fama da matsananciyar matsalar tattalin arziki, inda fiye da kashi uku na al'ummar kasar ke rayuwa a kasa da kangin talauci, sannan rashin aikin yi ya kai kashi 10%, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ta zarce kashi 54% a cikin shekara guda.