1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Minista ya ajiye aiki a Ajantina

Abdul-raheem Hassan
July 3, 2022

Ajiye aikin ministan ya zo ne a dai-dai lokacin da kasar ke fama da durkushewar tattalin arziki da ya shafi hauhawar farashin kayayyaki da matsanancin karancin man dizel da takin zamani da faduwar darajar kudin kasar.

https://p.dw.com/p/4DZkN
Ajantina
Martin Guzman, ministan tattalin arzikin Ajantina da ya yi murabusHoto: Martin Zabala/Xinhua News Agency/picture alliance

Ministan Tattalin Arzikin kasar Ajantina Martin Guzman ya yi murabus daga mukaminsa, sai dai har yanzu tsohon ministan da ya fara aiki tun 2019 bai bayyana dalilansa na daukar wannan mataki ba. Amma a wasikar barin aikin da ya aikewa shugaban kasa Alberto Fernandez, ya shawarci gwamnati ta dinke barakar cikin gida don kar wanda zai gaje shi ya sha irin wahalar da ya sha.

A matsayinsa na ministan tattalin arziki, Guzman ya jagoranci sake tattaunawa kan bashin dala biliyan 44 (€42.19) da asusun lamuni na duniya IMF, wanda Argentina ta dage cewa ba za ta iya biya ba.

Murabus din Guzman ya zo ne a dai-dai loakcin da Ajantina wacce ke zama kasa ta biyu wajen fitar da masara a duniya, kuma ta daya a fitar da waken soya da abinci da aka sarrafa amma ta fada matsalar tattalin arziki da ya shafi faduwar darajar kudin kasar da kuma hauhawar farashin kaya da karancin man diszel da taki.