Zaɓen 2011 a Najeriya
April 12, 2010Muƙaddashin shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi alƙawarin shirya zaɓe bisa gaskiya da adalci a shekara ta 2011 a wannan ƙasar ta Najeriya mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka. Jonathan wanda ke ziyarar aiki a birnin Washington na Amirka, ya faɗawa majalisar hulɗa da ƙasashen waje ta Amirka cewa wannan shi ne babban burin da ya ke son cimma a cikin shekara guda. Ya ce yanzu haka yana fuskantar babban ƙalubale a rayuwarsa ta siyasa. Shi dai muƙaddashin shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan wanda ya fara jan ragamar mulkin Najeriya bayan da shugaban ƙasa Umar Musa 'Yar Adua ya tafi neman magani a Saudiya a watan Nuwamban bara, ba ya da isasshen lokaci don tinkarar matsalolin da suka yiwa Najeriya katutu wato kamar rashin tsaro, rigingimun addini da kuma rashin shirya zaɓe na gaskiya.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala