1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin Taliban na karbe iko

Ramatu Garba Baba
August 12, 2021

Dubbai sun fada cikin matsanancin yanayin rayuwa a daidai lokacin da mayakan Kungiyar Taliban ke samun nasara a wani yunkurin son kwace iko daga hannun gwamnatin Afghanistan.

https://p.dw.com/p/3yvEJ
Afghanistan Taliban Konflikt l Vertriebene Familien aus dem Kundus, Kabul
Hoto: Wakil Kohsar/AFP

Wasu kasashen Turai sun yanke shawarar dakatar da mayar da 'yan kasar Afghanistan da suka nemi mafaka gida a sakamakon munin fadan da ake da mayakan Taliban. Rahotannin na cewa, a cigaba da yunkurinta na mamaye Afghanistan kungiyar ta karbe iko da binrin Ghazni birni na biyu mafi girma da ke Kudu maso yammacin Kabul.

Masu sharhi dai na ganin faduwar birnin Ghanzni mai tazarar kilo mita 150 kacal daga birnin Kabul, ka iya zama wata kafa ta shigar 'yan kungiyar zuwa Kabul babban birnin Afghanistan.