1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taliban na kara barazana a Afghanistan

Ramatu Garba Baba LMJ
August 9, 2021

Mayakan Taliban sun kwace iko da babban birnin Kundus da ke arewacin kasar, tare da kwace iko da muhimman gine-ginen gwamnati.

https://p.dw.com/p/3ylac
Afghanistan | Konflikte | Kundus in Händen der Taliban
Mayakan Taliban na ci gaba da kai munanan hare-hare da kwace yankunaHoto: Abdullah Sahil/AP Photo/picture alliance

Rahotanni daga Afghanistan din dai, sun tabbatar da yadda mayakan Taliban suka mamaye wasu manyan biranen da ke arewacin kasar. Bayan kame larduna uku a farmakin da suka kaddamar kan rundunar gwamnati, yanzu gundumar Kundus da a baya ke hannun gwamnati ta fada hannunsu. Ana dai ganin da wuya rundunar gwamnatin ta yi galaba kan mayakan, wadanda suka kwashe tsawon lokaci suna kokarin kwace mulki.

Karin Bayani: Taliban ta tsagaita wuta a Afghanistan

Sai dai kuma gwamnatin Afghanistan da ke fuskantar gagarumar barazana daga mayakan, ta ce tan dab ta karya lagon Taliban din. A yayin da Taliban ke kwace iko da yankunan, haka hare-harenta ke salwantar da rayuka. Dubban mutane na tserewa, zuwa kasashe da ke makwabtaka da Afghanistan din. Amma ga kasar da fiye da rabin al'ummarta ke fama da talauci barin muhallinsa ba shi ne mafita ba, sai dai fatan samun zaman lafiya. 

Afghanistan | Konflikte | Kundus in Händen der Taliban
Al'ummar Afghanistan, na fatan yin sulhu da TalibanHoto: Abdullah Sahil/AP Photo/picture alliance

Duk da kazancewar rikicin da rashin tabbas da al'ummar Afghanistan suka tsinci kansu, kaso da dama na da fatan ganin an ceto kasar daga durkushewa. An kwashe shekaru da dama ana kokarin shawo kan rikicin kasar, wanda har ya sanya rundunar kawance da Amirka ta jagoranta shiga Afghanistan din domin ganin ta taimaka wa gwamnati. Sai dai bayan shekaru 20, ana ganin rundunar kawancen ba ta cimma nasara ba. Daga bisani ma, Amirkan da rundunar tsaro ta NATO sun yanke shawarar ficewa daga kasar.

Karin Bayani: 'Yancin mata a sulhun Amirka da Taliban

Wani batu da ya bar baya da kura shi ne, rayuwar dubban 'yan kasar da suka yi wa sojojin kasashen yamman aikin tafinta da sauran aikace-aikace na cikin tsaka mai wuya bayan ficewar rundunar ba ta re da sun taimaka musu kamar yadda suka dauki alkwarai ba. David Richards wani tsohon shugaban rundunar sojojin Britaniya ne, ya  kumanemi gwamnatin kasarsa ta yi wa wadannan mutane  adalci. A halin yanzu dai ba ta sauya zani ba, domin kuwa kungiyar Taliban na kara fadada ikonta a yankuna da dama tare da kai munanan hare-hare ba kakkautawa.