1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sharhi a kan makomar Afirka ta Kudu bayan zabe

June 3, 2024

A karon farko cikin shekaru 30 da suka gabata jam'iyyar ANC mai mulki ta rasa rinjayen kafa gwamnati ita kadai a Afirka ta Kudu tun bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata a shekarar 1994.

https://p.dw.com/p/4gbGN
Shugaba Cyril RamaphosaHoto: Kyodo/picture alliance

Sakamakon zaben na karshe na Afirka ta Kudu ya nuna jam'iyyar ANC (African National Congress) ta samu fiye da kashi 40 cikin 100 na kuri'un da aka kada, abin da ya nuna gagarumin gibi daga kashi 57 cikin 100 da jam'iyyar ta samu lokacin zaben shekara ta 2019.

Lokacin kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata dajam'iyyar ANC take da karfinta, karkashin Marigayi Nelson Mandela ta lashe larduna uku cikin tara na kasar da gagarumin rinjaye, yayin da jam'iyya ta biyu a zaben DA (Democratic Alliance) take ci gaba da samun nasara a lardin yamamcin Cape. Amma ficewar tsohon shugaba Jacob Zuma wanda ya yi mulki daga 2009 zuwa 2018 daga jam'iyyar ANC da kafa jam'iyyar MK ya kassara karfin ANC a lardin Kwazulu Natal.

Südafrika |  Parlamentswahl 2024 | John Steenhuisen
Shugaban Jam'iyyar DA John SteenhuisenHoto: Themba Hadebe/AP Photo/picture alliance

Gwede Mantashe shugaban jam'iyyar ANC mai mulki ya dora alhakin rashin sa'ar jam'iyyarsa kan tsohon shugaban Jacob Zuma wanda ya fice daga jam'iyyar kuma ya janye kuri'u masu yawa daga jam'iyyar:

"Zuma tsohon shugaban ANC ya fice daga cikinta, sannan ya janye mata kuri'u da dama, kuma sakamakon ya nuna wannan rabuwar."

Hatta lardin Gauten da ke zama cibiyar kasuwancin kasar da ya kunshi birnin Johannesburg da Pretoria cibiyar mulki, jam'iyyar ANC ta fuskanci koma baya.

Südafrika | Parlamentswahl 2024 - MK Leader Jacob Zuma
Shugaban jam'iyyar MK Jacob ZumaHoto: Thuso Khumalo/DW

Shi ma Julius Malema tsohon shugaban matasa na jam'iyyar kuma jagoran jam'iyyar EFF mai neman sauye-sauyen tattalin arziki da jam'iyyarsa ta samu kusan kashi 10 cikin 100 na kuri'un da aka kada, ya bayyana shirin aiki tare da jam'iyar ta ANC mai mulki:

"Muna son aiki da ANC, idan akwai wata jam'iyya da za mu iya aiki tare mai yiwuwa ita ce ANC. Saboda idan ANC ta sassauto ba wani abu ba ne."

Ana bukatar samun rinjaye fiye da kashi 50 cikin 100 kafin kafa gwamnati, abin da ya saka tilas jam'iyyar ANC ta nemi abokan hulda, kuma jam'iyyar DA wadda ta samu fiye da kashi 21 cikin 100 a zaben, ta samu kari daga zaben da ya gabata, tana iya shiga kawancen.

Südafrika | Parlamentswahl 2024 - EFF leader Julius Malema
Shugaban jam'iyyar EFF Julius MalemaHoto: Thuso Khumalo/DW

Kawo yanzu jam'iyyar DA wadda take a matsayi na biyu a zaben na Afirka ta Kudu ta ce ba ta tantance mataki na gaba ba a hukumance, kamar yadda Solly Malatsi mai magana da yawun jam'iyyar ta DA ya yi karin haske lokacin tattaunawa da tashar DW:

"Ba a fara tattaunawa a hukumace ba tukunna, mu jira babban taron kwamitin gudanarwar jam'iyyar DA, domin daukar matsayi na gaba."

Yanzu dai tilas jam'iyyun siyasan na Afirka ta Kudu su nemi matsaya gabanin bude sabuwar majalisar dokoki cikin makonni biyu bayan sanar da cikakken sakamakon zabe kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.