Gwamnatin kawancen a karon farko a Afirka ta Kudu
May 31, 2024A karon farko za a kafa gwamnatin kawance a kasar Afirka ta Kudu shekaru 30 tun bayan komawa tsarin dimukaradiyya na duk jam'iyyu, sakamakon yadda aka rasa samun jam'iyyar da ta samu fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Bayan kirga fiye da kashi 52 cikin 100 na kuri'un zaben 'yan majalisar dokokin kasar, jam'iyya mai mulki ta ANC tana da kusan kashi 42 cikin 100 na kuri'un da aka kirga
Ita dai jam'iyyar ANC mai mulki Afirka ta Kudu ta shafe shekara 30 kan madafun ikon kasar, tun lokacin zaben farko, bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekarar 1994. Jam'iyyar DA ta galibi Turawa ta zo na biyu a zaben da kashi 23 cikin 100, sannan a matsayi na uku akwai jam'iyyar MK ta tsohon Shugaba Jacob Zuma da kashi 10 cikin 100, yayin da EFF ta Julius Malema take da kashi 9 cikin 100 a mastayi na hudu.
Tuni jam'iyyar ta bayyana goyon baya ga Shugaba Cyril Ramaphosa, wanda yake neman wa'adi na biyu na mulki, duk da rashin nasara da ta fuskanta lokacin zabe.