1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar JNIM ta dauki alhakin kai hari mafi muni a Benin

Binta Aliyu Zurmi AMA
January 11, 2025

Harin ta'addancin da ya kashe gwamman sojojin a jamhuriyar Benin ya kasance irinsa mafi muni a tarihi kasar mai iyaka da Nijar da Burkina Faso, duk da yake tana cikin barazanar hare-haren 'yan ta'adda shekaru da dama.

https://p.dw.com/p/4p3lM
Sojojin Benin na sintiri don tabbatar da tsaro
Sojojin Benin na sintiri don tabbatar da tsaroHoto: Marco Simoncelli/DW

Kungiya da ke da alaka da al-Qaeda ta JNIM ta dauki alhakin harin ta'addanci da aka kai a arewacin kasar Benin mai iyakar kasar da Burkina Faso da Nijar, harin da ya hallaka sojoji 28 a tsakiyar wannan makon.

Karin bayani : Kemi Seba zai tsaya takara a Benin

Harin da ke zama mafi muni da sojojin kasar Benin din suka gani a baya-bayan nan na zuwa ne, a daidai lokacin ma'aikatar tsaron Benin ta kara yawan sojojin da ke sintiri kan iyakar kasar da makwabtanta irinsu Nijar da Burkina Faso, wanda suka jima suna fama da ayyuklan ta'addanci.

A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar JNIM mai alaka da al-Qaeda ta bayyana hallaka sama da sojoji 30 tare da kwace bindigogi da jirage marasa matuka da tankokin yaki.

Karin bayani : Benin: Kokarin sasanta rikici da Nijar

Wata majiya daga kasar ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar daga shekarar 2021 ya zuwa watan Disambar 2024 sama da sojoji 120 ne 'yan ta'adda suka kashe a kasar.