1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin sasanta rikicin Nijar da Benin

Salissou Boukari LMJ
June 24, 2024

A wani mataki na neman warware rikicin da ya kunno kai tsakanin Jamhuriyar Nijar da makwabciyarta Jamhuriyar Benin, tsofaffin shugabannin kasar Benin na shirin zuwa birnin Yamai domin tattaunawa da hukumomin Nijar.

https://p.dw.com/p/4hRmS
Benin | Thomas Boni Yayi | Sulhu | Nijar
Tsohon shugaban kasar Benin homas Boni YayiHoto: Facebook/Präsident Patrice Talon

Tsofaffin shugabannin kasar Jamhuriyar ta Benin sun kudiri aniyar zuwa birnin Yamai ne, domin ganin ko za a samu mafita a rikicin da yaki ci yaki cinye wa tsakanin kasashen biyu makwabtan juna da har yanzu kan iyakokinsu ke a rufe. Manyan mutanen biyu sun ce za su je Nijar ne  domin ganawa ta musamman da hukumomin kasar su kuma bayar da gudunmuwarsu wajen sake kulla kyakkyawar alaka da 'yan uwantaka da moriyar juna da magabatan da suka shude na kasashen biyu kamar Hubert Maga da Hamani Diori suka kulla tare da kiyaye su. Kyakkyawar alaka da zamantakewar da suka ce magadansu wato Sourou Migan Apithy da Justin Ahomadégbé da Seyni Kountché da Ali Saibou da Mahamane Ousmane da Mamadou Tandja da Mathieu Kérékou da Nicéphore Dieudonné Soglo da Boni Yayi sunyi, wadanda duka lokacin mulkinsu sun yi kokarin rike wannan dangantaka.

Nijar | Benin | Rikici | Kan Iyaka
Dubban 'yan kasuwa da ma al'umma rikicin Benin da Nijar ya shafaHoto: AFP/Getty Images

Tuni dai wasu daga nasu bangaren ke ganin shiga tsakanin mataki ne mai kyau, idan bai saba da batun 'yancin kan Nijar ba. A kwanakin baya dai wasu yan asalin kasar ta Benin da ke zaune a birnin Yamai fadar gwamnatin Jamhuruyar ta Nijar, sun yi wani zama tare da fitar da sanarwa da bayar da shawarwari kan yadda ya kamata a warware wannan matsala ta hanyar amfani da tsofaaffin shugabannin kasashen biyu. Tsofaffin shugabannin biyu sun yi imanin cewa akwai bashin da ya kamata su biya na dattawan da suka gabace su, domin ci gaba da wannan zaman lafiya da aka kwashe shekaru ana yi. Tsofaffin shugaban kasar na Jamhuriyar Benin wato Soglo da Yayi sun gayyaci al'ummar Nijar da Benin din 'yan uwan juna da su ci gaba da addu'a, domin raka wannan kyakkyawar manufa tasu ta neman mafita.