1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan ta'adda sun kashe sojoji a Jamhuriyar Nijar

September 29, 2023

Gwamnatin kasar Nijar ta tabbatar da mutuwar sojojinta a wani harin ta'addanci da aka kai kansu a yankin kudancinta. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a kan iyaka.

https://p.dw.com/p/4WwaK
Sojojin Nijar da ke yaki da 'yan ta'adda
Sojojin Nijar da ke yaki da 'yan ta'addaHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Wasu mayakan tarzoma a yankin kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar, sun halaka sojojin kasar akalla bakwai a wani harin da suka kai kansu a jiya Alhamis.

Bayanai sun ce wasu karin sojojin na Nijar biyar ma sun mutu, a hadarin mota da suka yi a lokacin da suke kokarin kai dauki a yankin da mayakan tarzomar suke a jiyan.

Mutuwar sojojin dai na zuwa ne lokacin da Faransa ke shirin janye mayakanta na kiyaye zaman lafiya a kasar, sakamakon bukatar hakan da gwamnatin soja a Nijar din ta yi.

Ministan tsaron kasar, Salifou Mody ya tabbatar da harin da aka kai sojojin kasar a yankin Kandadji a yankin Tillaberi.