1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hari ya halaka sojoji a Nijar

February 11, 2023

Hukumomi a Nijar sun tabbatar da cewa wani harin ta'addanci ya halaka kimanin sojin kasar 10 a kan iyakar Nijar da kuma makwafciyarta Mali.

https://p.dw.com/p/4NNJO
Wani jami'in sojin Jamhuriyar Nijar
Wani jami'in sojin Jamhuriyar NijarHoto: ISSOUF SANOGO/AFP

Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar, ta tabbatar da mutuwar kimanin sojoji 10 yayin da wasu 13 suka jikkata a wani harin kwantar bauna da 'yan ta'addda suka kai musu a yankin Kudu maso Yammacin kasar. Ma'aikatar ta ce ta yiwu adadin wadanda suka mutu a harin ya karu, kasancewar har kawo yanzu akwai mutane 16 da ba a san inda suke ba a harin da ya afku a kan iyakar kasar da makwabciyarta Mali mai fama da rikici.