1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan siyasa na neman mukamai a gwamnatin Tinubu

May 11, 2023

Kasa da makonni uku kafin rantsar da sabuwar gwamnati, hankalin 'yan siyasa na Najeriya na karkata ga neman warware matsalolin kasar zuwa ga samun madafan iko, lamarin da ke zaman alamun dawowa daga rakiyar talakawa.

https://p.dw.com/p/4REB6
Zababben shugaban Najeriya Bola Tinubu da mataimakinsa Kashin ShettimaHoto: Ben Curtis/AP Photo/picture alliance

Jam'iyyar APC ta zo a cikin sunan fata a zaben 2023, kuma ta yi alkawarin sauya rayuwa ta 'yan kasa a wa'adinta na gaba. Sai dai a yanzu hankali na ta karkata a bangaren masu takama da siyasa a cikin tarrayar Najeriyar ya zuwa neman damar taka rawa a fagen iko na kasar. 

Shi kansa sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ke shirin hawa gadon da ya sa kafa ya fice zuwa Faransa cikin neman hanyar samar da gwamnati. Su kuma gwamnonin da ke shirin barin gadon suna hankoron rikidewa zuwa ministoci da ragowa na masu karfin ikon fada a ji ko ba dadi. A daya bangaren, 'yan doka na ta hankoron kaiwa ga shugabancin majalisun tarrayar Najeriyar guda biyu.

Nigeria Wahlen 2023
Talakawan Najeriya na neman zababben shugabaTinubu ya share musu hawayeHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

A yanzu dai,  fagen siyasar Najeriyar ya rude a yunkurin neman hanyar kaiwa ga gwamnati. Sai dai a cikin tsakiyar rudanin, an boye sunan talaka balle a nemi hanyar cika  alkawarin da ke tsakanin bangarorin guda biyu. Dr Umar Ardo da ya zage tudu da gangaren Adamawa a fatan zama gwamna na jihar, ya ce abun da ya ce ba wani fata a bangaren talakawan da ke hankoron inganta rayuwa.

A al'adance dai, lokacin da ke akwai na zaman na kokarin neman hanyoyin kaiwa ga warware jahilcin da ma talaucin da ke zaman  ruwan dare a ko'ina a tarrayar Najeiryar a halin yanzu. Sai dai a fadar Buba Galadima da ya taka rawa a zabukan bana, talakawa na kasar na zaman ummul aba'isan gaza kaiwa ya zuwa cika alkawarin da ke tsakaninsu da masu siyasar da ke da al'ada ta yaudara.