'Yan sandan Najeriya sun ɓace
August 24, 2014Talla
Wannan dai ya faru ne bayan da Ƙungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai a yankin arewa maso gabashin ƙasar ta kai farmaki a makarantar horar da 'yan sanda da ke garin Gwoza a jihar Borno. Rundunar 'yan sandan ƙasar ta sanar da cewar wannan shi ne karo na uku da ƙungiyar ke kai mata farmaki cikin wannan wata na Agusta a jihar ta Borno da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar da yake fama da rikici. Tuni dai sabon shugaban 'yan sandan ƙasar Suleiman Abba ya umurci da a tsaurara matakan tsaro a yankin.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hasane