1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin 'yan jarida a rikicin manoma da makiyaya

August 30, 2023

A kokarin magance rikicin makiyaya da manoma a Najeriya, cibiyar horar da 'yan jarida ta DW Akademie ta yaye sabon zubi na 'yan jarida daga kafafen yada labarai a Najeriya

https://p.dw.com/p/4VioG
Taron horar da 'yan jarida da sashen horaswar DW ya shirya a Najeriya
Taron horar da 'yan jarida da sashen horaswar DW ya shirya a NajeriyaHoto: Kano Nigeria/DW

Rikici tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya ya dauki lokaci yana tasiri ga rayuwar al'umma da fasalin labarai duba da salo da ma kalmoman da kafafen labaran cikin ke taka rawa wajen ta'azarar rigingimun da ke da ruwa da tsaki da sauyin yanayi.

To sai dai kuma wani horo na cibiyar horarwar DW ta shiya na tsawon watanni uku yana ta kokarin sauya tunanin dillallan labaran a cikin neman mafita kan rikicin da ma sulhu a tsakanin bangarorin biyu.

Kafafen labarai guda shida da yan jaridu 12 ne suka karade tuddai da kwari na jihar Gombe, kafin dawowa a Abuja da nufin nazarin yanayin noma da na kiwo da ma hanyoyin kaucewa rikici a tsakanin sana'o'in guda biyu.

Horon mai taken hanyar zaman lafiya 

Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Jamus ce ta dauki nauyin gudanar da shi, kuma a fadar Janine Stolpe dake zaman jagora, shirin na da babban burin mayar da kafafen labarai a matsayin jakadun zaman lafiya da kare barkewar rikicin manoma da makiyaya mai hadari.

Mahalarta taron 'yan jarida kan rikicin manoma da makiyaya a Najeriya
Mahalarta taron 'yan jarida kan rikicin manoma da makiyaya a NajeriyaHoto: Kano Nigeria/DW

"Suna taka rawa mai tasiri, saboda kowane dan jarida daga kowace kafa na yada bayanai, kuma in suka yada bayanai na tsana alal-misali to akwai matsala babba, saboda haka yake da muhimmanci a yada bayanan zaman lafiya, kuma a nemo masalaha cikin kowane batu. Muna fatan mai da masu halartar wannan horo jakadun zama na lafiya da za su yada bayanai a ko ina cikin kasa."

Karin Bayani: Plateau: Magance rikicin manoma da makiyaya

Kafafen yada labaran da suka ci moriyarar taron DW

Kafafen labarai guda uku na Platinun FM dake a Abuja da kuma Progress Radio ta birnin Gombe da Freedom dake biranen Kano da Kaduna ne suka yi nasarar tsallake zagaye na karshe na horarwar. Ibrahim Isma'ila na zama daya a cikin mahalarta horon daga kafar Platinum dake a Abuja, ya ce sun amfana da taron " A turance ana yawan fadin fulani herdsman, ana karkata abun ga wata kabila guda daya, wanda kuma abun ba haka yake ba, ko'ina a Najeriya kabilu da yawa na kiwo, kuma wannan kalma ta Fulani herdsman daga yanzu in naga wani na amfani da ita zan ce ya sauya, saboda ba fulani kadau ba ne suke yin kiwo, daga yanzu maimakon a ce fulani makiyaya, sai dai a ce makiyaya kawai. Saboda ba su kadai ba ne suke da shanu ko kuma suke yin kiwo."

Tasirin sauya fasalin kiran Fulani makiyaya zuwa makiyaya kawai

Idan har sauyin kalmomi suna shirin sauya da dama cikin sauya tunani al'ummar kasar, ga Aisha'a Adams Jalo dake aiki da kafar Progress dake a Gombe, kokarin neman mafita maimakon yaduwar rigingimun ne zai dauki hankalinta cikin batun dangantaka ta bangarorin gida biyu, kuma ta ce " Zan fi mayar da hankali kan samo mafita ga matsalar ba wai kawai yaduwar matsalar ba. Kuma ina jin 'yan jarida suna iya kawo karshen rikicin saboda su ne madubin al'umma tun da su ne masu yada rikice-rikice tsakanin al'umma."

Karin Bayani:  Rikicin Fulani da Makomar kiwo a Najeriya

'Yan jarida sun dukufa wajen nazari kan makomar rigingimu tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya
'Yan jarida sun dukufa wajen nazari kan makomar rigingimu tsakanin manoma da makiyayaHoto: Kano Nigeria/DW

in har cibiyar horaswar ta DW ta yi nasarar sauya tunanin 'yan jarida kamar su Ashi'a bisa rigingimun makiyaya da manoma, ga haruna Ibrahim idris na kafar Freedom ya fuskanci gagarumin sauyin aikinsa na jarida bayan a yayin horaswar dake zaman irin ta ta farko a cikin tarrayar Najeriyar, yana mai cewa "Bayan na shiga tawagar horaswar DW Academy na fahimci cewar yanda muke daukar labarin ma ba mu dauko hanyar magance matsalar ba. Amma ta dalilin wannan tawaga Alhamdu-Lillahi na samu abubuwa da dama tun ma daga dauko labarain har zuwa yada shi. In Allah ya yarda na samu ilimi daban-daban wanda zai inganta ya kuma canja tunanina ba iya makiyaya da manoma ba har ma daukacin al'umma gaba daya."

An kammala taron horaswar tare da wata muhawara ta kwarraru ,da ma ragowar jama'ar cikin gari ta kafar sadarwar Facebook kan hanyoyin warware matsaloli a tsakanin makiyaya da manoma.